Babban lauyan gwamnatin tarayya kuma ministan shari’a, Lateef Fagbemi ya yi kira da a soke hukumar zaɓen jihohi masu zaman kansu.
Da yake magana a wurin wani taron tattaunawa da aka gudanar ranar Litinin Fagbemi ya ce kamata ya yi a mayar da aikinsu hannu hukumar zaɓe ta ƙasa INEC.
Majalisar wakilai ce ta shirya taron tattaunawar da ya mayar da hankali kan samar da ingantaccen shugabanci da inganta matsalar tsaro a matakin ƙananan hukumomi.
Fagbemi ya ce gwamnonin suna amfani da wani naƙasu da wani sashen kundin tsarin mulkin 1999 inda suka mayar da ƙananan hukumomi basu da tasiri.
Ya ce gwamnonin suna amfani da hukumomin zaɓen wajen ɗora mutanen da suka ga dama akan mulkin ƙananan hukumomin ta hanyar yin zaɓe marar inganci.