Minista ta rankaya asibiti a kan keke don ta haihu

[ad_1]

Ta wallafa hotunanta tare da mijinta a Instagram rike da kekunansu.

Hakkin mallakar hoto
Julie Genter/Instagram

Image caption

Ta wallafa hotunanta tare da mijinta a Instagram rike da kekunansu

Ministar harkokin mata a kasar New Zealand ta rankaya asibiti a kan keke domin ta yi haihuwarta ta fari.

Ta haihu ne bayan cikin nata ya kai mako 42.

Minista Julie Genter ta jam’iyyar The Green Party ta ce ta ruga asibitin ne a kan keke domin a taimaka mata ta haihu saboda “babu sarari a cikin motata”.

Ta wallafa hotunanta tare da mijinta a Instagram rike da kekunansu.

A watan Yuni, Firayi Ministar kasar Jacinda Ardern ta zamo shugabar gwamnatin wata kasa ta biyu da ta haihu tana kan mulki. Dukkan matan biyu na zuwa asibitin Auckland City Hospital wanda kowa da kowa ke zuwa.

Ms Genter, mai shekara 38, wacce kuma take rike da mukamin ministar sufuri, ta yi fice wajen rajin hawa keke.

[ad_2]

More News

An kama wasu mutane biyu da hodar ibilis a Lagos

Rundunar ƴan sandan jihar Lagos ta sanar da kama wasu mutane biyu da aka samu ɗauke da ƙunshin hodar ibilis mai yawan gaske. Mai magana...

Ƴan sanda sun kama wani mutum ɗauke da bindigogi 20 a Kaduna

Rundunar Æ´an sandan jihar Kaduna ta ce jami'anta sun kama wani  riÆ™aƙƙen mai safarar bindiga inda aka same shi da bindigogin AK-47 Æ™irar gida...

Kwankwaso ya bada tallafin miliyan ₦50 ga mutanen da ambaliyar Borno ta shafa

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam'iyar NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bada tallafin naira miliyan 50 ga mutanen da ambaliyar ruwa a...

Sakamakon NECOn 2024 ya fito

Hukumar shirya jarabawar ta kasa ta fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare ta watan Yuni/Yuli 2024, inda kashi 60.55 cikin 100 na waÉ—anda suka...