Mimiko zai tsaya takarar shugaban kasa a jam’iyar Labour

Tsohon gwamnan jihar Ondo, Olusegun Mimiko ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a shekarar 2019.

Mimiko ya ce zai tsaya takara a karkashin jam’iyyar Labour Party (LP).

Ya bayyana aniyar tasa ranar Laraba lokacin da ya ziyarci ofishin jam’iyar na kasa dake Abuja.

Toshon gwamnan ya ce idan suka cigaba da tsayawa a gefe to kashe dake faruwa a yankin arewa ta tsakiya da kuma wasu sassa na kasarnan zai iya mamaye kasar baki daya.

Ya kuma kara da cewa matsalar tattalin arziki da ake fama da ita a yanzu tamkar somin tabi ne kan abinda zai faru anan gaba.

Mimiko ya mulki jihar Ondo na tsohon shekaru 8 karkashin jam’iyar LP kafin ya koma jam’iyar PDP.

Ya kuma sake komawa jam’iyar ta Labour a shekarar 2018.

More News

Ƴansanda sun kama muggan ƴan fashi da makami

Jami’an hukumar ‘yan sanda reshen Elemoro reshen jihar Legas sun kama wasu mutane uku da ake zargi da hannu a fashi da makami a...

An kama wasu mutane biyu da hodar ibilis a Lagos

Rundunar ƴan sandan jihar Lagos ta sanar da kama wasu mutane biyu da aka samu ɗauke da ƙunshin hodar ibilis mai yawan gaske. Mai magana...

Ƴan sanda sun kama wani mutum ɗauke da bindigogi 20 a Kaduna

Rundunar Æ´an sandan jihar Kaduna ta ce jami'anta sun kama wani  riÆ™aƙƙen mai safarar bindiga inda aka same shi da bindigogin AK-47 Æ™irar gida...

Kwankwaso ya bada tallafin miliyan ₦50 ga mutanen da ambaliyar Borno ta shafa

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam'iyar NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bada tallafin naira miliyan 50 ga mutanen da ambaliyar ruwa a...