
Hakkin mallakar hoto
Reuters
An dakatar da kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta Ajentina Lionel Messi daga buga wasanni na kasa da kasa har tsawon wata uku bayan da ya ce gasar kwallon kafa ta Copa America gurbatacciya ce.
An ba Messi mai shekara 32 da haihuwa jan kati a wasan da Ajentina ta buga da Chile wanda Ajentinan ta lashe da ci 2 – 1, kuma daga baya ya yi ikirarin “an murde gasar ne domin Brazil ta lashe kofin.”
Kungiyar Kwallon Kafa ta nahiyar Amurka ta Kudu Conmebol ta kuma ci shi tarar dala 50,000.
Amma Messi na da damar dauka karar dakatarwar da Conmebol ta yi masa nan da kwana bakwai.
Wannan na nufin Messi ba zai sami damar buga wa Ajentina wasannin sada zumunta da za ta buga da kasashen Chile, da Mexico da Jamus ba kenan a watannin Satumba da Oktoba.
Kasar za ta fara buga wasannin shiga gasar cin kofin duniya na shekarar 2022 a watan Maris na 2020.
- Messi na cikin ‘yan takarar gwarzon Fifa na bana
- Messi ya sha kashi a Copa America
Bayan da Brazil ta doke Ajentina da ci 2 da nema a matakin daf da na karshe, hukumar kwallon kafa ta kasar ta nuna damuwarta dangane da abin da ta kira “kura-kurai da alkalan wasan suka tafka masu tayar da hankali”.
A nata bangaren , Conmebol ta kare kanta, inda ta ce sukar da ake ma ta ba su da tushe kuma sun kasance tamkar “rashin girmamawa ne” a gareta.
An kori Messi a minti 37 na wasan da kasarsa ta buga da Chile, bayan sun kaure da dan wasa Gary Medel wanda shi ma an kore shi daga filin wasan.
daga bay Messi ya ce “Ba za mu bar wannan gurbataccen tsarin ya shafe mu ba. Sun nuna mana rashin mutunci tun farkon wannan gasar.”
“Abin takaici ne cewa gurbacewar, da alkalan wasan sun hana mutane shakatawa, sun bata shirin kawai.”