Meng Hongwei: Shugaban Interpol ya yi batan dabo

Shugaban Interpol Meng Hongwei
Shugaban Interpol Meng Hongwei

Jami’an ‘yan sanda a Faransa sun fara wani bincike kan bacewar shugaban hukumar ‘yan sanda na duniya wato Interpol.

Tun ranar 25 ga watan Satumba ba a kara jin duriyar Meng Hongwei – wanda dan kasar China ne ba – bayan da ya bar birnin Lyon shalkwatar hukumar ta Interpol akan hanyarsa ta zuwa China.

Ana ganin hukumomin China ne suka tsare shi.

An dai nada Meng Hongwei mai shekara 64 ga mukamin shugaban Interpol shekara biyu da ta wuce, kuma ya koma birnin Lyon da zama tare da matarsa da kuma ‘ya’yansa. Uwargidansa ce ta sanar da hukumomi cewa ya bace tun ranar 25 ga watan Satumba.

Jami’an ‘yan sanda na Faransa sun tabbatar da ya shiga jirgin sama daga Faransa zuwa China, amma akwai rahotannin da ke cewa hukumomin China ne suka kama shi, jim kadan bayan saukarsa daga jirgi.

Babu wanda ya san dalilin da China ke tsare da shi, amma ana ganin lamarin na da nasaba da alakar da yake da ita da wani tsohon ministan China wanda hukumomin Chinar suka kora daga aiki, kuma an yanke masa hukuncin daurin rai-da-rai sabili da laifukan cin hanci da rashawa.

Kawo yanzu dai gwamnatin China ba ta ce uffan ba game da wannan lamarin mai daure kai.

Kafin Mista Meng ya zama shugaban hukumar ta Interpol a shekarar 2016, ya rike manyan mukamai a ma’aikatar tsaron cikin gida ta China, kuma wa’adin shugabancinsa a hukumar Interpol zai kare ne a shekara ta 2020.

More from this stream

Recomended