Mece ce Fassarar “Baƙonka Annabinka” Zuwa Turanci?

Wani ya yi tambaya game da ma’ana tare da fassarar wannan karin magana da Hausawa ke cewa “Baƙonka annabinka.” To sai dai ba dole ba ne a samu lafazi a Turanci wanda kai-tsaye zai dace da shi domin harsunan biyu suna da matuƙar bambanci dangane da al’adu da tunaninsu – kamar yadda masana harshe suka tabbatar cewa ba a raba harshe da al’ada da tunanin mutane masu harshen.

Duk da haka, a fannin ilimin fassara, akwai wasu dabarbaru da ake amfani da su wajen fassara lafazi da ba a samunsa a harshen ƙarba (wato target language a Turance). Saboda haka, mai fassara zai yi iya ƙoƙarinsa wajen ganin cewa ya yi lafiyayyar fassara wacce ba za ta kautar da ma’anar lafazin da yake son fassarawa ba.

Duba da wannan bayani, ni a tawa fahimtar, za a iya fassara lafazin “Baƙonka annabinka” zuwa Turanci ya koma “Your visitor deserves your kindness.”

Muhammadu Sabiu

More from this stream

Recomended