Me ye alfanun samar da kudin bai-daya a ECOWAS?

Taron ECOWAS a Abuja

An dauki lokaci kasashen kungiyar ECOWAS na tattauna yadda za su samar da kudin bai-daya kamar irin tsarin na Tarayyar Turai.

Sai dai wasu na ganin ana ta jan kafa ga burin samar da tsarin da wasu ke ganin zai habaka tattalin arzikin kasashen na yammacin Afirka.

Wasu kuma na ganin yanayin kasuwancin bai-daya a irin yanki na Afirka babban jan aiki ne, musamman shakku da ake nunawa game da sharudda da kuma yadda za a aiwatar da yarjejeniyar ta kudin bai-daya tsakanin kasashen na Afirka.

An sake tattauna batun a taron shugabannin na ECOWAS da aka gudanar a Abuja a ranar Asabar amma ba tare da samar da wani ci gaba ba.

A taron na ECOWAS wasu sun bayyana damuwa game da yadda hada-hadar kasuwanci tsakanin kasashen yankin ke raguwa duk shekara.

Wannan ya sa wasu kasashen kungiyar ke kara matsa lamba don ganin an amince da tsarin kudin na bai-daya da suke ganin zai saukaka harkokin kasuwanci da bunkasa tattalin arziki.

Kalla Hankurau ministan harkokin waje na Jamhuriyar Nijar daya daga cikin kasashen da ke da’awar bullo da tsarin na kudin bai-daya, ya shaida wa BBC cewa suna bukatar gaggauta samar da tsarin domin zai bunkasa tattalin arzikin kasashen na ECOWAS.

Najeriya mafi yawan al’umma a Afirka kuma kasa ta biyu a karfin tattalin arziki, na daga manyan kasashen da ke baude wa kudirin.

Amincewar Najeriya yana da matukar amfani, saboda matsayin tattalin arzikinta a Afirka.


Kasashen Afirka sun fi hulda da kasashen yammaci fiye da makwabta
Wakilin Majalisar Dinkin Duniya a Afirka ta yamma Chambas Mohamed Ibn Chambas ya shaidawa BBC cewa samar da kudin na bai-daya zai kawo ci gaba a tsakanin kasashen yammacin Afirka.

“Muna rokon wadanda suke diba wannan magana da su yi sauri su kammala aikinsu domin ganin an fito da kudi na bai-daya a Afirka ta yamma,” in ji shi.

Ya ce idan akwai kudi daya a ECOWAS batun cin kasuwa da kasuwanci, a tashi daga Najeriya zuwa Senegal da Burkina Faso zai rage satar kudade.

Irin wannan bukatar dai ta dauki kungiyar Tarayyar Turai shekaru da dama.

Ga dorewar tsarin, dole sai ya kasance an gudanar da mafi yawancin kasuwancin tsakanin kasashen na Afirka.

Masharhanta na ganin wannan shi ne babban kalubalen da za a fuskanta, domin yawancin kasashen Afirka sun fi hulda ne da kasashen waje maimakon makwabtansu na nahiyar.

Kasuwanci tsakanin kasashen Afirka bai wuce kashi 16 ba duka. A tsakaninsu da kasashen yankin Asiya kuma kashi 51, a Turai kuma adadin ya kai kashi 70.

Hakan ya nuna yana da wahala kasuwancin na bai-daya ya karbu cikin lokaci kankani.

More from this stream

Recomended