Me ya sa matan Najeriya marsa auren ke wahalar samun gida?

[ad_1]

Yinka Oladiran

Hakkin mallakar hoto
Duru Azubuike/Duru Studios

Image caption

Yinka Oladiran ta ce masu bada haya sun fi so su ga mace tare da namiji.

Masu ba da haya da dama a Najeriya na zargin cewa, matan da suke neman haya alhali ba su da aure karuwai ne.

Wata mata mai shekara 30 da ke da babban aiki Olufunmilola Ogungbile, ba ta taba tunanin cewa za ta shafe wata biyar tana kwana a gidan kawarta ba, yayin da take neman gida a birnin Abeokuta a kudu maso yammacin Najeriya.

Ta koma Abeokuta ne daga Lagos bayan ta samu wani aiki mai tsoka daga gwamnatin jihar Ondo a matsayin babbar jami’ar wani shiri. To amma duk da cewa tana da kudi sosai, ta sha wahalar samun gidan da za ta zauna saboda ba ta da aure.

Ta ce “Tambayar farko da mai gida zai yi miki shi ne ko kina da aure?” Inji Ogungbile, “sai in ce musu ‘ba ni da shi’, sai ki ji sun ce to mai ya sa?

A mafi yawan lokutan abin yana daure mata kai.

“Me ya hada batun aurena da gidan da zan zauna?”

Muna son kamilallun mutane ne

Ms Ogungbile ta ce matsalar ta wuce duk yadda ake tunani.

“Kaso casa’in da tara cikin masu bayar da haya in na je wajensu ba sa son ba ni gida, saboda ba ni da aure,” kamar yadda ta shaidawa BBC.

Ta kara da cewa, “mafi yawancin wakilan masu ba da hayar suna ce min, ‘Za ki iya zuwa da saurayinki ko da mijinki?’ A irin wadannan gidajen, ba ma so mu ga samari suna shigowa barkatai. Muna so mu ga kamilallun mutane.”

Hakkin mallakar hoto
Gloria Yusuff

Image caption

Mafi yawan masu gidajen haya ba sunz zaton mata ba sa samun kudin da za su iya biyan haya.

Mis Ogungbile na ganin cewa matsalar da ta fuskanta tana da dangantaka ne da al’ada, inda ake daukar aure a matsayin wani ma’auni na kamewar mace.

“A wannan yankin, idan ba ki da aure to kawai ana daukar ki a matsayin karuwa,” a cewar ta.

Sylvia Oyinda -wata mai shago a Lagos – na da ra’ayin cewa irin wannan kallo da ake yi wa matan da ba su da aure ne ya sa suke wahalar samun gida a Najeriya.

An yi wa Ms Oyinda, mai shekara 31 baiko lokacin da ta ke neman gida. To amma an ki ba ta haya in ba ta je da saurayinta ba.

Maza sun fi kudi

Ms Oyinda ta ce irin wannan kallon masu gidajen haya suke yi wa mata.

“Masu gidajen haya uku na hadu da su, kuma sun ki nuna min gidajensu, suna ce min kar in damu,” in ji Oyinda

A karshe dole ala tilas ta daina yawon neman gida ita kadai, ta fara zuwa da saurayinta, wanda a yanzu suka yi aure, kuma da zuwa aka dauke ta da muhimmanci.

A yanzu ma’auratan na zaune a a wani gida mai daki hudu a unguwar Lekki.

Coleman Nwafor, Wani dillali kuma mai gidan hanya, ya ce shi ba ya nuna bambamci, sai dai mafi yawancin wadanda ya ke mu’amala da su wajen haya ko sayen gidaje maza ne, saboda sun fi kudi.

“Mafi yawancin ‘yan matan da suke zuwa neman gida suna karkashin iyayensu ne ko kuma samarinsu. Ba ka san me zai faru ba bayan shekara guda. Sannan su kuma masu gidajen haya sun fi son wadanda za su ringa biyan kudin haya ba tare da jinkiri ba,” kamar yadda ya shaidawa BBC.

Masu gidan haya suna sa wa mata ido

Yinka Oladiran mai shekara 25, wacce ta koma Lagos daga birnin New York a 2016 domin neman aikin gidan talabijin, ta ce ta zauna ba mai sa mata ido a Amurka, kuma tana so ta samu irin wannan ‘yanci a Najeriya.

Hakkin mallakar hoto
Gloria Yusuff

Image caption

Masu bada haya suna fi amincewa da mata da miji.

Tana kuma so ta rage yawan tafiyar da ta ke yi inda take shafe sa’o’i uku kafin ta je wajen aiki daga gidan iyayenta, to amma ta kasa samun gidan haya har sai da mahaifinta ya nuna amincewa.

Daga karshe dai hakarta ta cimma ruwa, bayan shafe wata shida tana neman gidan.

Sai dai ta ce a ko yaushe tana fuskantar raini daga masu gadin gidan, musamman idan ta makara ba ta koma gida da wuri ba, har a wasu lokutan su kan tambaye ta wajen wa ta zo?

“Farurwar hakan a kai a kai raini ne,” a cewar Oladiran.

To amma a wajen Ogungbile, wahalarta ta wata biyar wajen neman gida ta zo karshe, domin kuwa a yanzu ta samu gidan da za ta zauna.

Ta ce ta samu gidan ne ta hanyar wani dillali wanda ya maida hankali kan hanyar samun kudinta, ba tare da ya damu da jinsinta ko aurenta ba.

[ad_2]

More News

Kwankwaso ya bada tallafin miliyan ₦50 ga mutanen da ambaliyar Borno ta shafa

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam'iyar NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bada tallafin naira miliyan 50 ga mutanen da ambaliyar ruwa a...

Sakamakon NECOn 2024 ya fito

Hukumar shirya jarabawar ta kasa ta fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare ta watan Yuni/Yuli 2024, inda kashi 60.55 cikin 100 na waÉ—anda suka...

Ƴan Najeriya na shan baƙar wahala—Janar Abdulsalami

Tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalami Abubakar, ya ce wahalhalun da ake fama da su a Najeriya na kara tabarbarewa, kuma rabon kayan agajin ba...

EFCC ta musalta cewa Yahaya Bello na tsare a ofishin hukumar

Hukumar EFCC dake yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa ta'annati ta ce tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello baya ya tsare a hannunta. A...