MC Tagwaye ya fice daga jam’iyar APC ya koma SDP

Shararren mai wasan barkwanci, Obinna Simon wanda aka fi sani da MC Tagwaye ya sauya sheƙa daga jam’iyar APC ya zuwa jam’iyar SDP.

Ya sanar da haka ne a cikin wani sako da ya wallafa a shafukansa na soshiyal midiya a ranar Juma’a inda ya ce ya ɗauki matakin ne biyo bayan ɗauki lokaci yana tuntubar makusantansa.

Ya ce bayan duba na tsanaki ya fahimci cewa jam’iyar APC ta kauce daga kan manufofin da aka gina ta akai na kyautatawa tare da bunƙasa rayuwar Najeriya.

A maimakon haka shugabannin jam’iyar da masu riƙe da mukami sun mayar da hankali wajen jefa masu ƙaramin hali a cikin halin wahala.

Ya yi kira da ƴan Najeriya dake da manufa irin tasa da su tsallako jam’iyarsu ta SDP .

More from this stream

Recomended