Mbappe zai ci gaba da zama a PSG, Juventus tana dab da kammala sayen Pogba | BBC News

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Dan wasan Faransa Kylian Mbappe ba zai tunzura ya bar Paris St-Germain a bazara ba saboda tasirin da cutar korona ta yi a harkokin samun kudin kungiyar, don haka dan wasan dan shekara 21 zai ci gaba da zama a kungiyar zuwa kakar wasa ta baɗi. (L’Equipe, via AS)

Juventus tana dab da kammala sake sayen dan wasan Faransa Paul Pogba, mai sheara 27, daga Manchester United kuma za ta yi amfani da Adrien Rabiot, mai shekara 25, don yin ƙasa da farashin Pogba. (L’Equipe, via Sunday Express)

Amma har yanzu kocin Real Madrid Zinedine Zidane bai karaya ba a yunkurinsa na dauko Pogba daga Manchester United. (Mundo Deportivo, via Star on Sunday)

Barcelona da Real Madrid suna son dauko dan wasan Borussia Dortmund Jadon Sancho amma Manchester United ta fi yin azama a yunkurin dauko dan wasan na Ingila mai shekara 20. (Athletic, via Star on Sunday)

A gefe guda, Chelsea tana shirin karɓo £48.5m daga Atletico Madrid a kan dan wasan Spaniya mai shekara 27 Alvaro Morata a bazarar da muke ciki – kuma za ta iya kashe kudin wajen sayo Sancho. (Sun on Sunday)

  • An dawo Bundesliga amma ba ƴan kallo
  • Makomar Jesus, Sane, Kroos, Weghorst, Vinicius, Torreira

Dan wasanBarcelona Lionel Messi ya yaba kan ƙwarewar dan wasan Inter Milan kuma dan kasar Argentina Lautaro Martinez, mai shekara 22, wanda aka ce kungiyar ta Spaniya tana zawarcinsa. (Sport, via Metro)

Kocin Club Bruges Philippe Clement ya ce yana sa ran dan wasan Najeriya mai shekara 22 Emmanuel Dennis, wanda ake rade radin zai koma Arsenal, Newcastle United ko kuma Wolves, zai bar kungiyar. (La Derniere Heure, via Birmingham Mail)

Tsohon dan wasanBarcelona da Spaniya Xavi yana shakkar cewa dan wasan Liverpool dan kasar Senegal Sadio Mane, mai shekara 28, da dan wasan Arsenal dan kasar Gabon mai shekara 30, Pierre-Emerick Aubameyang, za su iya buga tamaula irin wacce ake murzawa a Nou Camp. (Metro)

Chelsea ta yi amannar cewa ta sha gaban Tottenham a yunkurinsu na dauko dan wasan Feyenoorddan kasar Netherlands mai shekara 16 Lamare Bogarde. (Football Insider)

More from this stream

Recomended