Mayakan ISWAP sun kashe sojoji da Civilian JTF a harin kwanton bauna

Mayakan kungiyar yan ta’addar ISWAP sun kai harin kwanton bauna kan jerin ayarin motocin dakarun sojan Najeriya da kuma Civilian JTF.

Lamarin ya faru ne a ranar Juma’a akan hanyar Damboa a wajejen Wajiroko dake jihar Borno.

Binciken da jaridar The Cable ta gudanar ya gano cewa mayakan na ISWAP sun kai hari kan ayarin ne lokacin da dakarun sojan suke safarar wasu kayan yaki ya zuwa wani wari.

Mayakan na ISWAP sun bude wuta kan ayarin lokacin da suke tsaka da tafiya akan titi abun da ya jawo musayar wuta a tsakanin bangarorin biyu.

A yayin musayar wutar ne aka kashe jami’an Civilian JTF biyu da kuma dakarun soja biyu.

Akalla baburan hawa guda 17 na sojoji mayakan na ISWAP suka yi awon gaba da su.

Tunda farko wasu labarai sun bayyana cewa mayakan na ISWAP sun dauke Birgediya Janar M.Uba dake jagorantar tawagar amma daga baya aka rundunar sojan Najeriya ta ƙaryata labarin inda ta ce tuni ya samu nasarar komawa sansanin sojojin.

More from this stream

Recomended