Mayakan ISWAP sun  kashe babban  jami’in soja a Borno

An kashe wani soja mai muƙamin manjo a Rundunar Sojan  Najeriya biyo bayan wani harin kwanton bauna da mayakan ISWAP su ka kai kan dakarun soja dake aikin sintiri a garin Damasak hedkwatar karamar hukumar Mobbar ta jihar Borno.

Wasu majiyoyi sun fadawa jaridar The Cable cewa babban jami’in sojan shine kwamandan sansanin soja dake Damasak  ya na jagorantar wasu sojoji su 30 dake aikin sintiri a kafa lokacin da suka fuskanci harin bindiga da kuma boma-bomai daga yan ta’addar.

Harin ya tilastawa sojojin watsuwa cikin  daji a yayin daga bisani 8 suka samu damar komawa sansaninsu.

Tun da farko dai an gaza gano 22 daga cikin sojojin ciki har da jagoran nasu.

” Daga bayanan da na tattara kwamandan sansanin sojan dake Damasak ya jagoranci aikin sintiri a kafa da ya ƙunshi dakaru 30 a ranar Juma’a amma suka fuskanci ruwan wuta daga mayakan ISWAP. Takwas ne kadai suka dawo sansanin a yayin da ba gano sojoji 22 ba a ciki har da kwamandan mai muƙamin manjo,” a cewar majiyar a zantawar da suka yi da jaridar The Cable.

Tun da farko rahotanni dake cin karo da juna sun bayyana cewa akwai yiyuwar yan ta’addar sun kama babban sojan bayan da wani  ya ke daga wayarsa a duk lokacin da sansanin ya kira shi.

Amma kuma wata majiyar dake jami’an tsaro ta yi watsi da raɗe-raɗin inda ta  ce an kashe babban sojan ne a musayar wuta a lokacin harin kwanton baunar.

More from this stream

Recomended