
Wasu ƴan bindiga da ake zargin mayaƙan kungiyar IPOB ne dake fafutukar kafa ƙasar Biafra sun kashe mutane biyar a jihar Anambra.
A cewar Zagazola Makama dake wallafa bayanai kan sha’anin tsaro a yankin tafkin Chadi an kai farmakin ne a ranar Alhamis lokacin da maharan suka dirar mikiya a wani gidan sayar da abinci dake kusa da kofar shiga Jami’ar Odumegwu Ojukwu dake Uli.
Bayanan da ya wallafa sun bayyana cewa kusan ƴan bindiga shida 6 ne suka isa wurin sai da abinci na Akuvic Kitchen a cikin wata bakar mota ƙirar Lexus da misalin ƙarfe 12:30 na rana inda suka buɗe wuta kan masu cin abinci ciki har da ƴan kungiyar AVG ta bijilante ta jihar Anambra.
Harin ya yi sanadiyar mutuwar, Okechukwu Iriakano mamba na AVG, Ifeanyi Esenwaka, wani mutum mai matsaikaicin shekaru, wani me hayar babur da kuma wata ƴar uwar me gidan abincin.
Kwamshinan ƴan sandan jihar Anambra, Nnaghe Itam ya kai ziyara gani da ido wurin da aka kai harin.