Mayakan Boko Haram sun kone kauyen Bwalakila dake Chibok

Bikin Kirsimeti ga al’ummar dake kauyen Bwalakila dake Chibok ya zo musu cike da bakin ciki bayan da yan ta’addar kungiyar Boko Haram suka kai hari kan kauyen.

Harin na Bwalakila na zuwa ne kwanaki guda bayan da yan ta’addar suka kai hari kan kauyen Makalama dake karamar hukumar ta Chibok.

“Yan ta’addar sun shigo ne daga Sambisa da misalin karfe 11 na dare ranar Kirsimeti inda suka kawo harin,”wani mazaunin yankin ya fadawa jaridar The Cable.

“Sun sace tare da kone duk abin da muke da shi.Bamu da abin da za mu ci bamu kuma da inda zamu yi bacci.Anyi harbi kan mutane da dama inda wasu suka samu raunuka.”

Ƙungiyar ta Boko Haram na cigaba da zafafa hare-hare akan garuruwa da kuma jami’an tsaro dake yankin arewa maso gabas duk da ikirarin da gwamnati take yi cewa ta ragargaza kungiyar.

More from this stream

Recomended