
Wasu da ake zargin mayakan kungiyar Boko Haram ne sun kashe wasu mutane a kauyuka uku dake fadin karamar hukumar Hong ta jihar Adamawa.
Mazauna wuraren da aka kai harin sun tabbatar da kai harin na ranar Litinin da daddare inda aka samu gano gawarwakin mutane 8 a yayin da ba a gano wasu mutum hudu ba.
Daya daga cikin wata majiya da ya nemi a boye sunansa ya ce maharan sun kai hari kauyen Zah, Kijing da Mubang.
“Mutane da dama na ganin yawan wadanda aka kashe zai iya haura 8 amma an lalata gidaje da dama a harin na daren ranar Litinin,” a cewar majiyar.
Amma kuma shugaban karamar hukumar Hong, Hon Inuwa Usman Wa’aganda ya ce kawo yanzu ya tabbatar da gano gawarwakin mutane 8 a kauyukan da abun ya shafa.
“An tilastawa mazauna Æ™auyukan da dama tserewa daga gidajensu domin neman mafaka,”
“Eh gaskiya ne Boko Haram sun kai hari Æ™auyukan Mubang, Zah da kuma Kijing ya zuwa gawarwaki 8 aka gano aaga Æ™auyukan uku a yayin da har yanzu ba a gano wasu huÉ—u ba,” ya ce

