
Mayakan kungiyar Boko Haram sun kai hari kan kauyen Makalama dake mazabar Gatamwarwa a karamar hukumar Chibok dake jihar Borno.
Harin na zuwa ne kasa da wata biyu da yan ta’addar suka kai hari kauyen Mifa dake garin na Chibok inda suka kashe dagacin kauyen.
“Sun zo da da daddaren nan (ranar Lahadi) ta kauyen Gogumdi dake kusa wanda yanzu babu kowa a ciki,”wani mazaunin Chibok ya shedawa jaridar The Cable.
“Sun fara harbi mutane suka fara gudu cikin daji.sojojin mu dake bataliya ta 117 suna shiryawa domin shiga su fatattake su,”ya ce.
Kauyen Makalama na da tazarar kilomita 21 daga garin Chibok.
Mai magana da yawun rundunar sojan Najeriya, Sani Usman Kukasheka ya tabbatar da faruwar harin inda yace jami’an sojan sun mayar da martani.