Mayaƙan ISWAP sun kashe kwamandan Boko Haram

Mayaƙan ISWAP sun kashe Gana Alhaji Ali kwamandan Boko dake lura da Sambisa da yankin Gwoza a tsaunukan Gwoza.

Wasu majiyoyi dake jami’an tsaro sun ce Ali na daga cikin hatsabiban mayaƙan Boko Haram a jihar Borno kuma an kashe shi ne a harin kwanton ɓauna da mayakan ISWAP suka kai a ranar Lahadi.

“Shi ne mataimakin Ali Ngulde idan ka ɗauke Abubakar Shekau babu wani mutum da ya kashe mutane kamarsa a dajin Sambisa, Banki da kuma bayan tsaunukan Gwoza.”

Majiyar ta ƙara da cewa yaransa sun dade suna saka fargaba da tsoro a zukatan manoma da kuma matafiya dake bin hanyar Pulka, Gwoza, Bama da kuma Mubi.

More from this stream

Recomended