Matsalar fyaɗe: An kama mutumin da ya yi wa ƴar shekara huɗu fyaɗe cikin masallaci a Bauchi

Bala Muhammad Gwamnan jihar Bauchi a Najeriya

Bayanan hoto,
Bala Muhammad – Gwamnan jihar Bauchi a Najeriya

Rundunar ‘yan sanda a garin Bauchi da ke arewacin Najeriya ta ce tana ci gaba da bincike kan wani mutum mai shekaru hamsin, da aka kama ana zargin ya yi wa wata yarinya ‘yar shekara hudu fyade a cikin masallaci.

Bayanai na nuni da cewa Jama’ar gari ne suka fara kama mutumin a masallaci tare da yarinyar, inda suka lakada masa duka kafin daga bisani ‘yan sanda suka shiga cikin lamarin.

A cikin ‘yan watannin dai ana samun yawaitar rahotannin fyade a Najeriya.

DSP Ahmad Muhammad Wakil ya fada wa BBC cewa tun ranar Alhamis ne suka kwaci mutumin daga hannun jama’a, suka kuma kai shi a kayi masa magani a asibiti.

Haka ma ya ce wannan ne karo na uku da aka kama mutumin da irin wannan ta’asa.

DSP Ahmad Muhammad Wakil ya ce a shekarun 2001 da kuma 2015 mutumin ya yi zaman gidan kaso na shekaru saboda kama shi da laifin fyade, kafin gwamnati ta yi masa afuwa.

Rundunar ƴan sandan na fata a wannan karon za a daukar wa mutumin mataki mai tsanani.

Ba a jima ba da gwamnatin jihar Bauchi ta kafa wata doka da ta kira VAPP wadda a turance ake kira Violence Against Persons Prohibition, ta kuma tanadi hukuncin kisa ta hanyar rataya ga duk wanda aka samu da laifin yi wa yara kanana Fyaɗe.

Haka ma dokar ta tanadi ɗaurin rai da rai ga wanda ya yi wa babbar mace fyaɗe, da kuma ɗaurin shekaru 20 ga waɗanda suka yi wa mace daya taron dangi.

Wannan dai na zuwa ne yayin da hukumomin ƴan sanda a jihar suka ce sun samu rahotannin aikata fyaɗe 21 a cikin watan Yuli kawai.

Me ke janyo fyaɗe?

Tsananin bukatar yin jima’i Likitoci sun ce wannan matsala na faruwa ne sakamakon ciwon ƙwaƙwalwar da ke damun mutanen da ke aikata fyaɗe.

Dr Attahiru Muhammad Bello, wani likitan ƙwaƙwalwa ne a hukumar kula da lafiya a matakin farko ta jihar Adamawa, kuma ya shaida wa BBC cewa matsalar gagaruma ce.

“Yawancin masu yi wa ƙananan yara fyaɗe suna fama da cutar da a Turance ake kira paraphilia, wato wata jarabar matuƙar bukatar yin jima’i, ko da kuwa da wani abu kamar ƙarfe ne ko kuma ƙananan yara,” in ji shi.

Ya ce a kasashen da aka ci gaba ana sanya musu ido idan aka ga suna nuna irin wannan ɗabi’u tun suna yara ta yadda za a riƙa yi musu magani tare da da ba su shawarwari.

Taɓin ƙwaƙwalwa – Dr Shehu Saleh shugaban asibitin kula da masu lalular ƙwaƙwala da ke garin Kware a jihar sokoto ya ce matsalar taɓin ƙwaƙwalwa na daga cikin dalilan da ke sa wasu su aikata fyaɗe musamman wadanda ba za su iya bambance abu mai kyau da marar kyau ba, kamar waɗanda ke aikata sata ko fashi da makami.

“Duk za su iya aikata fyaɗe saboda ba su san cewa laifi ne suka aikata ba, saboda ƙwaƙwalwarsu ta juye.”

Sai dai Likitan ya ce yawancin masu aikata fyaɗe dama ce suka samu tsakaninsu da waɗanda suke yi wa fyaɗen da kuma mugun halin da ke ransu.

Ya ce akwai hanyoyi da dama da mutum zai bi ya biya bukatarsa ta samun gamsuwa amma saboda mugun halin da ke ransu ke sa su aikata yin fyaɗe.

Likitan ya ce fyaɗe na iya jefa yaran da aka yi wa cikin damuwa kan mugun abin da aka aikata masu, wanda zai iya shafar ƙwaƙwalwarsu.

“Babban matsalar fyade shi ne yaran da aka yi wa fyaden, yana janyo masu taɓin hankali har ta kai su ma suna yi wa wasu fyaden,” in shi Dr Shehu Saleh.

Mene ne fyade?

Bayanan hoto,
Ana samun karuwar mata da kananan yara da ake cin zarafinsu ta hanyar fyade

Dakta Nu’uman Habib, masanin halayyar dan Adam ne a Jami’ar Bayero da ke Kano kuma a cewarsa, “fyaɗe yana nufin haike wa mata, wani sa’in ma har maza ba tare da izininsu ba, ba tare da sahalewarsu ba, ba tare da yardarsu ba.”

Dakta Nu’uman ya ce tasirin fyaɗe na da girma musamman a rayuwar yara, don kuwa ya kan daɗe a kwakwalwarsu kuma ya jefa su cikin damuwa da tsoro da rashin yarda da amincewa.

“Duk wanda suka haɗu da shi sai su yi tsammanin mai irin wannan halayyar ne. Kuma damuwar takan daɗe tare da su a cikin kwakwalawarsu kusan ta sa ma su sukurkuce”, a cewarsa.

Sai dai bisa alama jama’a ba su gane haka ba, don kuwa ba a cika tattauna batutuwan da suka shafi fyade ba, bare a bai wa wanda a ka yi wa taimakon da ya dace.

Idan aka yi wa wata ko wani fyaɗe, shi da iyalansa sukan zage dantse su tabbatar mutane ba su sani ba. Wannan ba ya rasa nasaba da ƙyama da ake nuna wa waɗanda aka yi wa fyaɗe da iyalansu.

Kuma wannan yana hana jami’an tsaro yin aikinsu yadda ya kamata, musamman ta fannin bincike da yanke hukunci ga wanda ya aikata laifin.

Abin da ya fi dacewa

Bayanan hoto,
An kaddamar da kundin rijistar ne don kawo karshen matsalar fyade a Najeriya

Hajiya Rabia Ibrahim, shugabar wata ƙungiya mai zaman kanta da ke ayyukan kula da mata da kananan yara da marayu a jihar Kaduna a Najeriya, mai suna ARRADA ta shawarci jama’a musamman iyaye kan yadda ya kamata su kula da kai komon ‘ya’yansu.

  • Ya kamata iyaye musamman mata su sanya ido kan masu kula da ƴaƴansu, misali direba ko kuma mai aiki.
  • Iyaye su kula sosai da mutanen da ƴaƴansu suke matuƙar shakuwa da su misali kawunni ko gwaggo ko anti da dai sauransu.
  • Kula da masu yawan yi wa yara wasa ko kuma ba su kyaututtuka.
  • Ka da iyaye su rinka korar ƴaƴaansu da su je su yi wasa domin ƙyale su don su shakata.
  • Iyaye mata su rinka duba al’aurar yaƴansu musamman idan suka zo suna kuka saboda ba su san komi ba.

More News

Gwamnan Kano ya sanya hannu kan dokar yin gwajin lafiya kafin aure

Gwamnan jihar Kano, Engr Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan wata doka za ta tilastawa masu yin aure yin wasu gwaje-gwajen lafiya gabanin...

An kashe kwamandan soji a Katsina

An kashe kwamandan sojoji na wani sansanin soji da ke Sabon Garin Dan’Ali a karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina a wani harin kwantan...

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...