Kamfanin Kaduna Refining and Petrochemical Company KPRC ya ce matatar mansa za ta fara aiki a shekarar 2024.
Mustapha Sugungun managan matatar man ta KRPC ne ya bayyana haka a ranar Litinin lokacin da ƴan kwamitin wucin gadi na majalisar dattawa kan man fetur ƙarƙashin jagoranci sanata, Ifeanyi Uba suka kai ziyarar aiki matatar.
Ya ce matatar man dake iya tace gangar mai 110,000 za ta fara aiki da kaso 60 na adadin da take iya ta cewa a ƙarshen shekarar 2024kafin daga bisani ta fara aiki ɗari bisa ɗari..
Sugungun ya ƙara da cewa aikin gyaran matatar da a yanzu aka kammala kaso 40 ana sa ran kammala shi a lokacin da aka saka.
A nasa jawabin Uba ya ce ziyarar aikin wani ɓangare ne na ƙoƙarin haɗin gwiwa tsakanin shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu da kuma majalisar ƙasa na ganin cewa dukkanin matatun ƙasar nan sun dawo domin kawo ƙarshen shigo da mai daga ƙasashen waje.