Matatar mai ta fatakwal za ta iya fara aiki a ƙarshen watan Yuni

Matatar mai ta Fatakwal mai tace mai ganga 210,000 a kowacce rana na iya fara aiki a karshen watan Yuli bayan dogon lokaci.

Jami’in hulda da jama’a na kasa na kungiyar ‘yan kasuwa masu zaman kansu ta Najeriya, Cif Ukadike Chinedu, ne ya bayyana sabuwar ranar.

Ya bayyana cewa, wannan ci gaban zai zaburar da harkokin tattalin arziki, rage farashin man fetur da kuma samar da wadataccen abinci.

A shekarar da ta gabata a cikin watan Disamba, Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur, Heineken Lokpobiri, ya sanar da kammala aikin tare da kaddamar da fara aikin babbar matatar man a Fatakwal.

More from this stream

Recomended