
Matatar man fetur ta Dangote ta rage farashin litar man fetur ya zuwa ₦865 kan kowace lita.
A cewar majiyoyi matatar man ta rage ₦15 kan kowace litar mai da take sayarwa da dillalan mai daga naira 880 da ta sayar da kowace litar a ranar Laraba.
Anthony Chijiena mai magana da yawun matatar ya tabbatarwa da jaridar The Cable labarin rage kudin sai dai ya gaza fadar sabon farashin.
Amma kuma Billy Gillis Harris shugaban kungiyar PETROAN ta masu gidajen sayar da mai ya faɗawa jaridar The Cable cewa “matatar ta rage farashin ya zuwa ₦865 kan kowace lita,”
Wannan cigaban da aka samu na zuwa ne kwana guda bayan da gwamnatin tarayya ta tabbatar da cewa za a cigaba da sayarwa da matatar ɗanyen mai akan farashin naira biyo bayan karewar wa’adin yarjejeniyar da suka cimma kan sayarwa da matatar ɗanyen mai tsakanin NNPCL da matatar Dangote