Matashiyar da ke hana mata zaman banza a Najeriya

open diaries

Miliyoyin matasa na fama da rashin aikin yi a Najeriya, yayin da ‘yan mata a nasu bangaren, ko da sun yi karatun boko ba duka mazajensu ne ke bari su yi aikin ofis ba, saboda wasu dalilai na al’ada da addini.

A yanzu an samu ci gaba kwarai wajen ilimin ‘ya’ya mata a arewacin najeriya, sai dai hakan bai sa an samu sauyi wajen su samu ayyukan yi ba.

Amma a wannan zamanin da dama zun yunkuro don yin sana’o’i maimakon zaman kashe wando.

Sai dai duk da haka akwai mata masu dumbin yawa da ba su da walwalar da za su iya koyon wata sana’a ko kuma su samu jarin farawa.

Amma ga dukkan alamu matasa irin su Fatima Fuad Hashim a shirye suke su bayar da irin tasu gudunmowar don kawo sauki kan wannan lamari.

Fatima wata matashiya ce mai shafin wallafe-wallafe a intanet da aka fi sani da Open Diaries, wadda ta dauki nauyin ‘yan mata 50 da ake koya musu sana’o’i daban-daban, ciki har da yin fanke da daukar hoto da kwalliyar mata ta zamani.

Abokin aikinmu Ibrahim Isa ya ziyarci wasu daga cikin cibiyoyin da ake horar da ‘yan matan a Kano, ya kuma ga yadda kwararru a fannoni daban-daban na sana’o’i karkashin tsarin Fatima suka zage suna koyar da dalibai a aikace.

Kimanin ‘yan mata 20 zuwa 30 ne suke sanya malamar kowane darasi a gaba, cike da fatan cewa a karshen darasi, kowacce za ta nakalci yadda ake abun da ake koya mata.

Mafi yawan masu koyon sana’o’in dai ‘yan mata ne daga wadda ta kammala karatun digiri a jami’a sai wadda ta yi karatu a makarantun gaba da sakandare, wadanda ke da yakinin cewa sana’a ta fi dogaro da aikin ofis, kasancewar za su iya tafiyar da sana’ar ko daga gidajensu.

Fatima ta ce ta fito da shirin horar da matan ne bayan ta fahinci kalubalen da suke fuskanta daga irin sakonnin da suke turawa ta shafin nata a Instagram.

Fatima tana daukar dawainiyar koyawa wadannan mata sana’a ne da kudin aljihunta da kuma tallafin da wasu bayin Allahn ke aikawa ta shafinta.

Yanzu dai ‘yan mata hamsin ne ke cin gajiyar horarwar, wadanda ake sa ran su ma za su koyar da na baya mutum goma-goma bayan an yaye su, kuma haka ake fatan ludayi zai yi ta kewayawa tsakanin wadanda za a dinga yayewa da sabbin zubi, don cimma burin shirin na dora mata a kan turbar dogaro da kai!

More News

Kwankwaso ya bada tallafin miliyan ₦50 ga mutanen da ambaliyar Borno ta shafa

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam'iyar NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bada tallafin naira miliyan 50 ga mutanen da ambaliyar ruwa a...

Sakamakon NECOn 2024 ya fito

Hukumar shirya jarabawar ta kasa ta fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare ta watan Yuni/Yuli 2024, inda kashi 60.55 cikin 100 na waÉ—anda suka...

Ƴan Najeriya na shan baƙar wahala—Janar Abdulsalami

Tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalami Abubakar, ya ce wahalhalun da ake fama da su a Najeriya na kara tabarbarewa, kuma rabon kayan agajin ba...

EFCC ta musalta cewa Yahaya Bello na tsare a ofishin hukumar

Hukumar EFCC dake yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa ta'annati ta ce tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello baya ya tsare a hannunta. A...