Connect with us

Hausa

Matashin da ke amfani da Tiktok don tattauna batun lafiyar ƙwaƙwalwa

Published

on

mace rike da waya kan gado

Asalin hoton, Alamy

Wani matashi mai suna Max Selwood, mazaunin Landan mai shekara 23 ya yi fice a manhajar TikTok, amma ba kamar abin da aka saba gani ba na raye-raye da koyar da abinci, wadanda su ne suka fi haska manhajar a duniya tun fitowarta a shekarar 2020.

Shi Selwood ya mayar da hankali ne kan harkokin da suka shafi kula da lafiyar ƙwaƙwalwa, wanda duk da cewa ba nishaɗi ba ne, yana da muhimmanci sosai.

Selwood, wanda ya kasance yana fama da matsalar fargaba da damuwa da ruɗu da rikicewar tunani, yana yin bidiyo ne a kan abubuwan da suka shafi fargabar shiga mutane, da ruɗu, jijji da kan maza da neman rigima da sauransu.

Ya fara saka bidiyo ne game da kula da lafiyar ƙwaƙwalwa a Instagram kimanin shekara uku da suka gabata, sannan ya fara TikTok kafin barkewar annobar Covid-19.

“A TikTok an fi samun matasa, sannan burina shi ne su fahimci cewa ba abun kunya ba ne don mutum ya shiga damuwa, sannan abun murna ne idan mutum ya shiga farin ciki.

“Sannan idan kana da wata matsala a ƙwaƙwalwa, ba laifi don ka yi magana a game da ita domin samun maslaha da wayar da kan al’umma,” in ji Selwood.

Sannan ya kara da cewa sanya bidiyoyin ya taimaka masa wajen gyara nasa tunanin da yanayi.

A kafofin sadarwa, matasa masu shekaru 6 zuwa 24 irinsu Selwood suna yawan tattauna batun lafiyar kwakwalwa.

Nuna damuwa

A wani bincike da Cibiyar Bincike ta Pew Research Center ta gudanara a shekarar 2018, ta gano cewa daya bisa ukun matasa masu shekarun 13 zuwa 17 suna bayyana damuwarsu a kafafen sadarwa na zamani ne.

Hakan ya fi yawa kuma a manhajar TikTok, inda matasa ne suke da kashi 60 na sama da mutum biliyan daya da suke amfani da manhajar a duniya.

A TikTok, Max Selwood yana sanya bidiyo game da yadda ya sha wahala da damumar kwakwalwa, da burinsa na ganin an daina ƙyamatar bayyana matsalar a fili

Wannan sabon salon na fitowa fili a bayyana kula da tunani ya zo a daidai lokacin da ake bukatarsa.

Lafiyar ƙwaƙwalwa ita ce babbar matsalar da ke addabar matasa, domin an fi samunsu da ita sama da dattawa.

A wani bincike da aka yi a shekarar 2020, an yi amfani da matasa 1,000 masu shekaru 18 zuwa 65, wanda kamfanin bincike na consumer data-research ya gudanar.

Kusan rabin mutanen sun ce suna da cikakkiyar lafiyar ƙwaƙwalwa, amma a ƙalla sau uku, yara masu shekara 6 zuwa 24 da matasa masu shekara 24 zuwa 40 sun ce suna fama da matsalar kwakwalwa idan aka kwakwanta su da dattawan.

A da, fitowa fili a yi bayanin lafiyar ƙwaƙwalwa abin kunya ne, amma a yanzu matasa sun fara fitowa fili suna yi ba tare da la’akari da kyamar da za a nuna musu ba.

Abin tambayar a nan shi ne, shin wane irin karfin zuciya matasan suke da shi da suka fito suna bayyana damuwarsu da mu ba mu da ita?

Masana sun ce yanayin zamani ne da ake ciki, amma kuma duk da haka, akwai wani karfin rai da matasan yanzu suke da shi.

Bayyana damuwa a fili

A gomman shekaru, yadda ake nuna ƙyama da wariya ga mutumin da ke fama da matsalar ƙwaƙwalwa ya sa mutane da dama sun ki fitowa fili su bayyana halin da suke ciki, wanda hakan ya sa ake samun koma baya wajen maganin matsalar a dattawa, musamman cutar damuwa da rudu.

A wani bincike da aka gudanar a shekarar 2019 a Birtaniya, an gano cewa wadanda da aka haifa jim kadan bayan Yakin Duniya na 2 ‘ba sa son magana akan lafiyar kwakwalwa.

“Ina tunanin dattawa da dama suna fama da matsalolin nan amma sun yi shiru” domin fargabar kyamar da za a nuna musu, inji Lisa Strohchein, Shugaban Sashen Kula da Jama’a na Canada kuma Farfesan Halayyar Dan Adam a Jami’ar Alberta.

Wadanda suka fara aiki yanzu suna da irin tunanin na fitowa su yi bayanin lafiyar kwakwalwa

Masu amfani da TikTok suna samun miliyoyin masu kallon batun na damuwa da OCD.

Yanzu manhajar TikTok ta zama wata kafa ta tattauna lafiyar kwakwalwa.

Ana alakanta kafofin sadarwa da kara matsalar kwakwalwa, amma abin mamaki, matasan nan suna amfani da su wajen gyara ga lafiyar kwakwalwar.

Manhajar TikTok ta samar da wani dandamalin da za a rika tattauna irin wannan batutuwa ne ta hanyar nuna kauna da lallama; a tsarin manhajar, wanda yake bidiyo ne da ake kallon juna, ya sa ana kaunar juna.

Masu amfani da TikTok suna samun miliyoyin masu kallon batutuwan da suke tattaunawa kan kula da lafiyar kwakwalwa.

A karshen shekarar 2020, an yi wani tsari a TikTok, inda mutum zai dauki kimanin minti 15 yana gwajin yanayin damuwarsa sannan ya ga sakamako.

Sannan akwai tsarin ba da shawara a manjahar ta TikTok, wanda shi ma yana tashe yanzu.

Duk da cewa wadannan tsarukan ba za su sama tabbatacce ba kasancewar ba kwararru ba ne su bayar, amma suna taimaka wajen bayani da wayar da kai.

Duk da cewa yara masu shekaru 6 zuwa 26 su ne aka fi jin muryarsu, masanan sun ce matasa masu shekarun 24 zuwa 40 sun taimaka wajen sauya tunanin mutane kan kula da lafiyar ƙwaƙwalwa.

Likitar kwakwalwa, B Janet Hibbs, ta ce matasa masu shekaru 24 zuwa 40 ne suka taimaka wajen yaƙi da nuna ƙyama ga masu fitowa fili suna bayyana lafiyar ƙwaƙwalwarsu.

Matsin tattalin arzikin shekarar 2008 da harin ta’addancin 9/11 ya kawo sauyi matuka a yanayin tunanin matasa masu shekaru 24 zuwa 40.

Sannan masana suna ganin suma yara masu shekara 6 zuwa 24 a yanzu annobar Covid-19 ce za ta sauya nasu tunanin.

Mene ne kalubalen?

Lallai akwai kalubale a cikin bayyana irin wannan damuwar a fili. Bincike ya nuna cewa ma’aikata da dama, musamman tsofaffi suna ɓoye bayanin lafiyar kwakwalwarsu.

Wasu ma suna tsoro ko za a dauke su aiki, ko kuma tsoron ka da a kyamace su a wajen aiki.

Amma Selwood ya ce bai damu da wadannan kalubalen ba, sannan bincike ya nuna cewa a cikin yara masu shekarun 6 zuwa 24 shi kadai ne ya amince da hakan.

Goyon bayan da Selwood ya samu daga mutane da ‘yan uwa, ya sa ya daina fargabar komai, har ma a wajen aiki. “Idan misali maigidana ya ce, “na kalla bidiyonka a TikTok.

Amma ya tabbatar cewa ba kowa ba ne zai iya fitowa fili ya bayyana lafiyar kwakwalwa.

Selwood yana aiki tare da masu taimaka masa wajen isar da sakonsa a kafofin sadarwa, kuma ya ce ya samu cikakken goyon baya.

Cire tsoro da fargabar ƙyama

Hibbs da Strohschein sun bayyana cewa akwai alamar za a samu cigaba a yadda ake tattauna batun lafiyar kwakwalwa kamar yadda matasa masu shekarun 24 zuwa 40 suka fara, sannan kannansu suka daura, wanda a cewarsu zai taimaka wajen jawo masu matsalar kwakwala da masu nakasa kusa.

Sun ce ana samun cigaba wajen rage yadda ma’aikatu ke nuna kyama ga masu fama da matsalar kwakwalwa, wanda annobar covid-19 ma ta taimaka wajen rage kyamar masu nakasa.

Haka kuma Selwood yana da kudirin ganin sauyin ya samu, sannan yana ganin kafofin sadarwa ne za su ja ragamar fafutikarsa na ganin an daina kyamatar bayyana lafiyar kwakwalwa a fili a shekaru masu zuwa.

Amma a yanzu, duk da cewa zai cigaba da fafutikar ce a intanet, ya ce “a karshe dai burina shi ne in taimaka. Idan mutum daya ya kalli bidiyona, sannan bidiyon ya taimako masa, to na yi farin ciki.”

Continue Reading
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending