Wasu matasa a birnin Kano sun kashe wani matashi da ake zargi da kisan ladanin wani masallaci, lamarin da ya tayar da hankula a unguwar Hotoro.
Rahotanni sun ce lamarin ya faru da safiyar Litinin, lokacin da ladanin masallacin, Zubairu Kasim, ke shirin kiran sallar asuba. An ce matashin ya shiga masallacin tare da makami, inda ya kai masa hari.
Da manema labarai suka kai ziyara wurin, an tarar da al’ummar yankin da ‘yan uwan mamacin suna cikin jimami bayan an kammala jana’izar ladanin.
Bayan harin, wasu daga cikin matasan unguwar sun tattaru, inda suka bi sawun wanda ake zargi da aikata kisan. A cewar Isa Kasim: “Allah ya yi shi ma wanda ya kai harin ba zai tsira ba, ƴan unguwa suka yi tara-tara har suka cimma wanda ya kashe shi, inda suka kashe shi, shi ma.”
Ya ƙara da cewa, “Bayan da ƴan unguwa suka kashe wanda ya kai harin, sai su ka ga maƙogwaron mahaifina a cikin aljihunsa a leda.”
Rahotanni sun ce matasan sun kuma ƙona gidan iyalan wanda ake zargi. Hukumomin tsaro sun tura jami’ansu yankin domin dawo da doka da oda bayan tashin hankalin da aka samu.
Matasa Sun Hallaka Matashin Da Ake Zargi Da Kisan Ladanin Masallaci A Kano

