Mataimakin gwamnan Bauchi ya musalta rahoton marin ministan harkokin waje

Auwal Muhammad Jatau mataimakin gwamnan jihar Bauchi ya musalta marin ministan harkokin waje na Najeriya, Yusuf Maitama Tuggar.

Ya fadi haka ne lokacin da yake mayar da martani kan wani rahoton da ba a tabbatar ba dake cewa ya farma ministan akan hanyarsu ta zuwa fadar Sarkin Bauchi wajen nadin sarautar tsohon gwamnan jihar, Muhammad Abdullahi Abubakar a matsaiyin Makama Babba I na masarautar Bauchi da kuma ɗaurin auren ƴarsa Khadija Muhammad.

Da yake magana ta bakin Muslim Lawal mai taimaka masa kan kafafen yaɗa labarai mataimakin gwamnan Bauchin ya ce ” A’a, a’a ta yaya  mataimakin gwamna zai mari minista? Bana tunanin hakan zai taɓa faruwa a Bauchi saboda nasan maigidana a matsayin shugaba mai kamun kai kuma mataimaki gwamnan Bauchi ba zai taba marin minista ba ko kuma wani mutum.”

“Bani da masaniyar haka yanzu nake ji a karon farko. Idan akwai wata sheda cewa mataimakin gwamnan ya yi haka zaka iya magana kan haka. Bamu san haka ba mataimakin gwamna ba zai iya haka ba wannan ce matsayar mu,” Lawal ya ce.

Duk ƙoƙarin jin ta bakin ministan ya ci tura.

More from this stream

Recomended