Matan daya bayan daya da su ka hada da shugabar mata masu zaman kan su ta Najeriya Amaka Naara sun gabatar da kan su da korafin an kama su ba bisa ka’ida ba.
Daya a cikin mata masu zanga-zangar mai suna Amaka ta ce “a kullum ‘yan sanda na kawo ma na samame a otal-otal da mata masu zaman kan su ko tarawa da maza a biya awalaja, su kan karbi kayyadedden kudi na goro a wajen mu don barin mu, mu yi sana’a.”
“Abin da ya ban mamaki shi ne jami’an sun caje mu da yawon banza, ni ban gane yadda hakan ya ke da ma’ana ko alaka da lamarin tara kudin shiga ba.
Ta kara da cewa a Lagos akwai ‘yan sanda da su kan biya kudi don a kyale su, kuma da zarar an yi sabon DPO sai a zo a damke su sai sun biya kudi ko kuma wani lokacin ‘yan sandan na neman kwanciya da matan kyauta ne.
Matan sun ce ‘yan sandan kan kama su su karbi kudi daga bisani su dawo su neme su, su na masu al’ajabin in har za a kama su mata me ya sa ba za a damke maza masu neman su ba.
Sun yi zargin bayan an tattara su, wasu da su ka kasa belin kan su, sun fada tarkon jami’an da su ka yi mu su fyade ba da kwaroron roba ba.