Mata 168 ake saka kowace rana a Saudiyya – Hukumomi

Sakin mata na karuwa a Saudiyya

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Wasu alkaluma da aka fitar na baya-bayanan sun nuna cewa ana sakin mata 58,000 a Saudiyya, wanda kashi 24% ne na aure 158,000 da aka yi a bara a kasar, kamar yadda jaridar Saudi Gazzette ta ruwaito.

Alkaluman da hukumar kididdiga ta kasar ta fitar sun nuna cewa a kowanne wata ana sakin mata 179 zuwa 253 a sassa daban-daban na kasar.

Ma’aikatar shari’a ta kasar ta ce kotunan kasar sun bada sharudan saki sau 4,688 a fadin kasar cikin watan Fabarairu, hakan ya rubanya alkaluman daga kashi 14% na sake-saken da ake yi a watannin baya.

Wannan yana nufin a duk sa’a guda ana sakin mata bakwai a Saudiyya.

Saki a aure kamar yadda kwararu a kan zantuttukan da suka shafi iyali ke cewa, ya kan faru ne idan duk wani kokari na shawo ko daidaita ma’aurata ya gagagra.

Mutuwar aure ko ma dai mecece ke haifar da ita, takan zo da dinbin matsaloli da ke tagayyara iyali.

Mutuwar aure ta fi tasiri ko shafar yara. Su kan girma a cikin wani yanayi da ke tasiri ga rayuwarsu.

Yara kan shiga cikin wani yanayi domin tamkar an sace masu walwala ne da fahimta da sanin dadi ko fuskantar gazawa a rayuwa.

Matan da ake sakin na shiga cikin wani yanayi da ke shafar kwakwalwa ko jefa su cikin matsin tattalin arziki. Suna iya rasa damar sake wani aure la’akari da karuwar ‘yanmata da mata masu shekaru da suka jima babu miji.

Mazan da ba su yi nasara ba a aurensu na farko na nuna fargabar sake aure musamman ga wadanda suka kashe makudan kudade a aurensu na farko.

Akwai dalilan saki ko mutuwar aure da dama.

Sai dai sukan danganci yanayin fahimta da al’ada da banbancin tunani tsakanin ma’aurata.

Rashin wayewa kan sanin muhimmancin iyali na daga cikin abubuwa da ke haddasa mutuwar aure, wanda ke faruwa akasari saboda rashin hakuri daga bangaren miji ko mata.

Kwararu sun yi kira kan bukatar bincike mai zurfi ko bayanai domin gano dalilan sakin aure da zummar samar da mafita.

Ire-iren wadannan bincike sun fito da bayanai karara, wadanda za a iya amfani da su wajen kawo karshen matsalar.

More News

An fara rushe wasu gine-gine 500 a kasuwar Karmo dake Abuja

Hukumar FCTA dake kula da birnin tarayya Abuja ta fara rushe gine-gine sama da 500 da aka yi ba bisa ka'ida ba a kasuwar...

Tinubu ya tarbi shugaban kasar Senegal Bassirou Faye a fadar Aso Rock Villa

A ranar Alhamis ne shugaba Bola Tinubu ya tarbi shugaban kasar Senegal Bassirou Faye a fadar Aso Rock Villa, a ziyarar da Faye ya...

NEMA ta karɓi ƴan Najeriya 150 da aka dawo dasu gida daga ƙasar Chad

Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Ƙasa NEMA ta ce ta karɓi ƴan Najeriya 150 da aka dawo da su bayan da su ka maƙale...

Ƙungiyar ƙwadago ta ƙi amincewa da ₦48,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi

Taron zaman ganawa da ƴan kungiyar ƙwadago da gwamnatin ta tarayya ta kira  ya tashi babu shiri bayan da wakilan kungiyar ƙwadago suka fice...