Gamayyar kungiyoyin ‘yan asalin babban birnin tarayya Abuja da kungiyoyin farar hula sama da 10,000 ne suka fito gaban majalisar dokokin kasar a ranar Laraba, inda suka yi kira da Nyesom Wike, ministan babban birnin tarayya, da ya yi mury.
Masu zanga-zangar sun nuna rashin cancantar Wike a matsayin daya daga cikin dalilansu na yin zanga-zangar.
A jawabinsa na taron, shugaban kungiyar Adamu Kabir Matazu, ya bayyana tsohon gwamnan jihar Ribas a matsayin maras kunya.
Matazu ya bayyana damuwarsu game da alkiblar babban birnin tarayya Abuja a karkashin gwamnatin Wike, inda ya ce abin da ya yi ya kawo cikas ga manufofin shugaba Tinubu ba, har ma ya sanya shakku kan sahihancin gwamnatin tarayya.