Masu teba na karuwa a yankunan karkara

Masu Kiba

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Wani cikakken bincike da akayi ya nuna cewa matsalar kiba na karuwa musamman a yankunan karkara a shekaru 30 da suka gabata wanda ya nuna cewa ba wai matsala ce ta mazauna birane kawai ba.

Mazauna yankunan karkara nauyinsu ya karu zuwa kilo biyar da rabi idan aka kwatanta da shekarar 1985, wanda ya ke yafi na mazauna birane nesa ba kusa ba.

Maza ‘yan kasar Sin da Amurka, su kibarsu ta karu ne da kilo tara.

Masu binciken wadanda suka yi amfani da alkaluma daga binciken da suka yi a kan mutane miliyan 12, sun ce karuwar arziki da kuma amfani da abincin da aka sarrafa na cikin dalilin da suke janyo karuwar matsalar kiba a duniya ma baki daya.

Ana kuma ganin cewa a cikin shekaru 40 da suka wuce matsalar ta ninka har sau uku.

Masu binciken sun ce binciken na su wanda aka wallafa shi a mujallar journal Nature, na nufin cewa wannan na bukatar a sake neman hanyoyin da za a sake magance wannan matsala.

More from this stream

Recomended