Masu garkuwa da wasu yara a Kaduna sun rage kuɗin fansar da za a biya ya zuwa miliyan 25

Masu garkuwa da ƙananan yara huɗu ciki har da ƙanƙanin yaro a jihar Kaduna sun rage kudin fansar da su ke so a biya su daga  naira miliyan 300 ya zuwa miliyan 25.

An sace yaran ne lokacin da babansu ya fita ranar Talata da daddare domin ya duba matarsa wacce take kula da jariranta ƴan biyu da aka kwantar a wani asibiti dake kusa da su.

Yaran an sace su ne daga gidansu dake unguwar Keke A a garin Millennium City dake ƙaramar hukumar Chikun ta jihar Kaduna kuma tun lokacin ne suke tsare a hannun masu garkuwar.

Daga bisani masu garkuwar sun tuntubi mahaifin yaran, Adamu Inusa inda suka bukaci a biya su miliyan ₦300 a matsayin kuɗin fansa tare da yin barazanar kashe yaran.

Ƴan fashin dajin sun kuma yi barazanar kashe ɗan ƙanƙanin yaron saboda yana damunsu da kuka.

A zantawar da ya yi da jaridar Daily Trust a ranar Litinin mahaifin yaran Adamu ya ce sun rage kudin fansar ya zuwa miliyan ₦25 kuma duk da haka bashi da halin biya.

More from this stream

Recomended