Masu garkuwa da mutane sun kashe shugaban APC bayan karbar kudin fansa miliyan 5

Masu garkuwa da mutane sun kashe, Nelson Adepoyigi shugaban jam’iyar APC na mazabar Ifon 5 a karamar hukumar Ose ta jihar Ondo.

A yan kwanakin da suka wuce aka dauke Adepoyigi daga gidansa dake Ifon.

Har ila masu garkuwar sun sako mutane biyu da suka rike lokacin da suka kai kudin  fansa miliyan 5 da kuma kayan abinci da suka bukata a kai musu kafin su sako marigayin.

Tunda farko masu garkuwar sun bukaci a biya naira  miliyan 100 amma daga baya suka yarda a biya su miliyan 5 bayan tattaunawa.

An bada rahoton cewa sun rike yan aiken da suka kai kudin fansar inda suka bukaci karin miliyan 30.

Clement Kolapo Ojo shugaban karamar hukumar Ose shi ne  ya tabbatar da mutuwar marigayin a cikin wata sanarwa da Oluwaseun Ogunniyi mai taimaka masa kan kafofin yada labarai ya fitar.

More from this stream

Recomended