Rundunar ƴan sandan jihar Kogi ta ce an kashe biyu daga cikin ɗaliban bim ɗaliban Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Confluence wato CUSTECH dake Osara a jihar Kogi.
A ranar 9 ga watan Mayu ne ƴan bindiga suka kai farmaki Jami’ar inda suka yi awon gaba da ɗalibai dai-dai lokacin da suke tsaka da yin karatun jarrabawa.
A ranar 14 ga watan na Mayu kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kogi, Kingsley Fanwo ya sanar da cewa an ceto 20 daga cikin ɗaliban a yayin da wasu huɗu suke hannun ƴan bindigar.
Da yake magana da Kamfanin Dillancin Labarai Na Najeriya NAN ranar Lahadi, Betrand Onuoha kwamishinan ƴan sandan jihar ya bayyana kisan ɗaliban da masu garkuwar suka yi a matsayin abun da bai dace ba.
Onuoha bai yi ƙarin haske ba kan batun amma ya ce jami’an tsaro na cigaba da bibiyar masu garkuwar.