Masu garkuwa da mutane sun kashe ƴan sanda biyu a Jos

Wasu ƴan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kashe ƴan sanda biyu a lokacin da aka ɗakile yin garkuwa da mutane wajen unguwar Rayfield dake ƙaramar hukumar Jos South dake jihar Filato.

Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar, DSP  Alabo Alfred shi ne ya tabbatarwa da manema labarai faruwar haka a Jos inda ya ce an kama mutane huɗu da ake zargin suna da hannu a yunkurin na yin garkuwa da mutane.

Mazauna yankin Little Rayfield sun faɗawa wakilin jaridar Daily Trust cewa sun ji ƙarar haribin bindiga a yankin da misalin ƙarfe 09:00 na daren ranar Talata a yankin.

Sun bayyana cewa masu garkuwar sun yi yunkurin yin garkuwa da wasu mutane amma kuma sai jami’an ƴan sanda suka daƙile shirin na su.

A cewar Alfred jami’an ƴan sandan da aka kashe sun zo jihar yin wani aiki ne na musamman daga Abuja.

More from this stream

Recomended