
Jami’an ƴansanda a jihar Edo sun kama wasu mutane bakwai ciki har da wasu samari biyu da ake zarginsu da sace wani mai suna, Osamagbe Atomon daga hannun mahaifinshi.
An kama mutanen ne a yankin Egor da Ekiadolor dake wajen birnin Benin ranar 25 ga watan Mayu.
Mutanen da ake zargi sun hada da Etinosa Ogbomo, shekara 22; Andrew Monday, shekara19; Edosa Ogierakhi, shekara 24; Efosa Aibueze, shekara 19; Evans Osazuwa, shekara 34; Sunday Felix, shekara 24 da kuma Ede Kingsley,mai shekara 20.
Jami’an rundunar dake yaki da garkuwa da mutane da kuma zamba ta Intanet sune suka samu nasarar kama su bayan wasu sahihan bayanan sirri da suka tattara.
Da yake magana da wakilin jaridar Daily Trust,mai magana da yawun rundunar yansandan jihar,Chidi Nwanbuzor, ya ce mutanen da ake zargi sun kai farmaki tare da kwace wani mai suna,Osamagbe Atoman daga hannun mahaifinshi suka kuma tsere cikin wata mota kirar Audi 80 tare da yaron kafin jami’an tsaro su kamo su.
Ya ce mutanen sun amsa laifin da ake tuhumarsu da aikatawa ya yin da aka mayar da yaron hannun mahaifinsa.
Kayan da aka samu wurinsu sun hada da bindigogi biyu kirar gida guda biyu, bindiga guda daya, harsashi goma,mota kirar Audi 80 da kuma babur.