Masu satar mutane a Najeriya sun fara fitowa baro-baro suna umurtar dangin wadanda suka kama da su biya su kudin-fansa ta banki.
Wannan alamari na faruwa ne a Abuja, babban birnin kasar.
Wani da ake sace `yar uwarsa a wannan watan, ya ce barayin ba su yi shayin ce masa ya saka musu kudin da suka nema a asusun banki ba.
“Mun daidaita da su a kan cewa zan biya naira 500,000 a matsayin kudin-fansa. Da na tambaye su ta wace hanya zan biya, sai suka ce ta banki. Suka ba ni lambar wani asusu a bankin access.
Daga nan sai na sanar da sashen `yan sanda masu yaki da masu satar mutane, inda jami`ansa suka ce na je na biya kudin. Daga nan sai na biya, sannan na kai musu shaida. Kuma ba da dadewa ba na tuntube su, amma sai suka ce suna ci gaba da binciken lamarin,” in ji shi.
Wannan lamari, kamar yadda masana harkar tsaro ke cewa, yana da hadari, kuma wajibi ne mahukunta su gaggauta daukar matakin dakile shi.
Duk da cewa jami`an tsaro na ikirarin cewa suna gudanar da bincike, masana fasahar sadarwa ta zamani na cewa bin-sawun irin wadannan barayi ba shi da wuya, in ji Injiniya Sale Gwani, wani kwararre a wannan fannin.
Ya cewa: “Kowane dan kansa wanda ya ke ya mallaki asusun ajiya a kowane banki sai da ya samu lamba wadda za a iya tabbatar da shi ne wanda ya mallaki wannan asusun ajiya. Wannan lamba ta kunshi bayanai na sa watau sunansa da wurin da aka haife shi da sauransu.”
“Kuma a duk lokacin da aka samu matsala na kan cewa miyagun mutane sun bukaci a saka kudi a wani asusu na banki, to idan aka saka kudin nan ya kamata a ce an sa ido domin a ga wanene zai zo ya cire kudin,” in ji shi
Shi ma masanin harkar tsaro, Dr Kabiru Adamu na kamfanin Beacon Consulting, ya bayyana cewa wannan salo da barayin mutanen suka fito da shi na karbar kudin-fansa ta banki ba shi da bambanci da yin fashi a tsakanin jama`a ido-na-ganin-ido, kuma bai kamata mahukunta su yi wasa lamarin ba saboda hadarinsa.
A baya dai, irin wadannan barayin kan karbi kudi ne lakadan, inda akan kai musu kai-tsaye ko ta hannun masu wakiltar su.
Yayin da mahukunta ke neman hanyoyin dakile matsalar satar mutane, masanan na cewa da zarar an samu hadin-kai tsakanin jami`an tsaro da hukumomin da ke yaki da masu aikata laifukan da suka shafi kudi, da kuma cibiyoyin da ke hada-hadar kudi, da wuya miyagu su sha idan sun yi damfara ko sun karbi kudin fansa ta banki.