Masu ƙwacen waya sun kashe wani matashi a garin Funtua

Wasu gurbatattun matasa masu ƙwacen waya sun kashe wani matashi mai suna, Ibrahim Muhammad a garin Funtua na jihar Katsina.

A cewar wani shedar gani da ido lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 05:30 na asubahi akan titin Danja dake unguwar Kasuwar Mata a birnin na Funtua.

Muhammad wanda aka fi sani da Elana ya fita sallar Asubahi a wani masallaci dake kusa lokacin da matasan suka biyo shi.

Sun  bukaci ya basu wayarsa amma yaƙi har ta kai su ga kokawa inda suka caka masa wuƙa   abun da ya yi sanadiyar mutuwarsa.

Tuni aka yi jana’izarsa ranar Talata da karfe 10:00 na safe kamar yadda addinin musulunci ya tanada.

More from this stream

Recomended