
Asalin hoton, Getty Images
Wani masanin wasanni Guillem Balague ya ce dan wasan da Arsenal ke son dauka Martin Odegaard ya zabi tafiya Real Sociedad domin buga tamaula aro.
Bayan da Nesut Ozil ke daf da komawa Fernerbahce, Gunners ta tuntubi Real Madrid kan daukar dan kwallon mai shekara 22 zuwa karshen kakar bana.
Odegaard ya ci karo da cikar da Real Madrid ba ta sa shi a wasa sosai kamar yadda ya kamata a bana.
Odegaard wanda aka yi hasashen zai yi fice a fagen tamaula a lokacin da ya koma Spaniya daga Stromgodset ta Norway yana da shekara 16 ya taka rawar gani a lokacin da ya buga wasannin aro a Sociedad.
Bayan da ya koma Real ne karkashin Zinedine Zidane wanda ya horar da shi a karamar kungiya aka dauka zai yi amfani da shi sosai.
An fara wasa biyu da shi a La Liga a bana, kuma rabonda Odegaard ya taka leda a gasar ta Spaniya tun 21 ga watan Nuwamba.
Ba Arsenal kadai ce da ke buga Premier League ke son daukar matashin dan wasan da ya gwammace ya je Real Sociedad ba, suna da yawa masu zawarcin sa.
Rabonda ya yi Real wasa tun ranar 1 ga watan Disamba, wanda ya yi minti biyar aka sauya shi, sakamakon raunin da ya yi.