Manchester City ta je ta doke Watford da ci 3-1 a wasan mako na 15 a gasar Premier League a Vicarage Road ranar Asabar.
Minti hudu da fara wasa Raheem Sterling ya fara ci wa City kwallo, kuma na 11 da ya ci Watford kenan, kuma irin yawan da ya zura a raga a haduwa da Bournemouth.
Bernado Silva ne ya zura na biyu da na uku a raga, kuma shida kenan da ya ci wa City a Premier League a karawa takwas – fiye da kwazon da ya yi a baya a fafatawa 61 a dukkan karawa.
Saura minti 16 a tashi daga wasan ne Watford ta zare kwallo ta hannun Juan Hernandez, wanda ya shiga karawar daga baya.
Da wannan sakamakon City ta koma ta daya a kan teburin Premier League da maki 35, bayan buga wasa 15.
Liverpool wadda ranar Asabar ta hau kan teburin, bayan cin Wolverhampton 1-0 da kyar da gumin goshi, yanzu ta koma ta biyu mai maki 34.
Chelsea wadda ta shiga wasannin mako na 15 a matakin farko ta koma ta uku a teburin babbar gasar Ingila da maki 33, bayan da ta sha kashi a gidan Wast Ham United da ci 3-2.
Karo na shida da David Moyes ya yi nasara a kan Chelsea a fafatawa 33 da ya yi da kungiyar a matakinsa na koci da yin nasara uku a West Ham daga ciki.
Kawo yanzu City ta yi nasara a kan Watford a karawa 19 da cin kwallo 62, rabon da Watford ta ci City a Vicarage Road tun 1985.