Man U ba ta son sayar da Pogba, Lukaku zai daina buga wa Beligium

[ad_1]

Paul Pogba

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Pogba ya koma United ne a shekarar 2016 a kan fam miliyan 89

Manchester United ta ce ba za ta sayar da dan wasan tsakiyarta dan Faransa, Paul Pogba, wanda yake son komawa Barcelona, in ji jaridar (Sun).

Ita kuwajaridarMirror ta ce Arsenal tana da kwarin gwiwar ci gaba da rike dan wasa tsakiyar Wales, Aaron Ramsey, mai shekara 27, duk da cewa Barcelonada Lazio suna son dan wasan.

KocinTottenham Mauricio Pochettino ya shaida wa (Sky Sports) cewa yana ganin wasu ‘yan wasan za su bar kulob din kafin a rufe kasuwar musayar ‘yan wasa duk da cewa Spurs ba ta sayi ko dan wasa daya ba a wannan lokacin bazarar.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Moussa Sissoko (a hagu)

Amma kuma (Talksport) ta ruwaito cewa dan wasan tsakiyar Tottenham,dan Faransa, Moussa Sissoko, mai shekara 29, ya shaida wa magoya bayan kulob din cewa shi zai tsaya a kungiyar.

Pochettino ya kuma ce yana shirin kasancewa da Tottenham na tsawon lokaci bayan ya samu damar koma wa Real Madrid, ko Chelsea a kakar da ta gabata, kamar yadda jaridar (Mirror)ta ruwaito.

Chelsea ta tattauna da dan wasan gaban kungiyarLyon,Nabil Fekir, mai shekara 25, a lokacin bazara, amma a lokacin bazara ta ki sayen dan kasar, Faransan, a cewar (Goal).

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Yaya Toure

Ita kuma jaridar (Sun) ta ambato kocin West Ham, Manuel Pellegrini, yana cewa kungiyarsa ba za ta sayi dan wasan tsakiyar Ivory Coast, Yaya Toure, mai shekara 35, wanda ya kasance ba shi da kulob, tun bayan da ya bar Manchester City.

Dan wasan gaban Manchester United dan kasar Belgium, Romelu Lukaku, mai shekara 25, ya ce yana son ya daina buga wa kasarsa kwallon bayan kammala gasar cin kofin kasashen nahiyar Turai ta Euro, wadda za a yi a shekarar 2020, in ji (Business Insider).

Real Madrid ba ta ji dadin cewa Inter Milan ta tuntubi dan wasanta na tsakiya dan kasar Croatia, mai shekara 32, Luka Modric, ba tare da fara tuntubar kulob dinsa ba, a cewar (Mundo Deportivo).

[ad_2]

More News

Zanga-zanga: An jibge Æ´an sanda 4200 a Abuja

Rundunar Æ´an sandan birnin tarayya Abuja ta tura Æ´an sanda 4200 gabanin zanga-zangar da za a gudanar a cikin watan Agusta. Kamar yadda masu shirya...

Kamfanin NNPC ya shirya daukar karin ma’aikata

Kamfanin mai na Nigerian National Petroleum Company Limited ya shirya daukar karin ma’aikata.Kakakin kamfanin na NNPC, Olufemi Soneye, ya tabbatar da hakan a wata...

Ya kamata matasa su yi haÆ™uri zanga-zanga ba ita ce mafita ba – Sarkin Zazzau

Sarkin Zazzau, Mai Martaba Ahmed Nuhu Bamalli ya ce matasa su ƙara haƙuri da gwamnatin tarayya su janye zanga-zangar da suka shirya gudanarwa a...

Zanga-zanga: Tinubu ya gana da gwamnonin APC

Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya gana da gwamnonin da aka zaɓa ƙarƙashin jam'iyar APC. Taron ganawar da aka gudanar a fadar shugaban ƙasa ta...