Mama Taraba Ta Zama Yar Takarar Gwamna Karkashin Jam’iyyar UDP

A daidai wannan lokaci da jam’iyun Najeriya ke fidda wadanda zasu tsaya musu takarar gwamna a jihohin kasar,yanzu haka tsohuwar ministan harkokin mata Senata Aisha Jummai Alhassan da akewa lakabi da maman Tarabata samu tsayawa a matsayin ‘yar takara a wata jam’iyya.

Tsohuwar Ministan wanda bata dade da ficewa daga jam’iyar APC ba ta lashe zaben fidda gwani da jam’iyar UDP ta gudanar,kuma tace bata shayin karo da maza,kamar yadda ta saba.

A jawabinta,Maman Taraba tace jam’iyar UDP, zata bada mamaki a babban zaben dake tafe,inda ma ko ta bayyana cewa.

Ko a zaben 2014, kotun daukaka kara ta baiwa Aisha Jummai Alhassan nasarar cewa ita ta lashe zaben jihar Taraban a inuwar jam’iyar APC,to amma kuma daga bisani kotun koli ta yi fatali da wannan hukunci tare da ayyana gwamnan jihar na jam’iyar PDP,Arc. Darius Dickson Isiyaku,DDI a matsayin gwamnan.

More from this stream

Recomended