Makomar Guardiola, Neymar, Messi, Mbappe da Ndombele

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Manchester City za ta sabunta kwangilar kocinta Pep Guardiola mai tsoka bayan ta yi nasara da karar da ta daukaka kan haramta mata buga gasar zakarun Turai. (Mirror)

Guardiola zai samu kudi kusan fam miliyan £150 domin karfafa tawagarsa. (Guardian)

Dan wasanNapolida Senegal Kalidou Koulibaly, mai shekara 29, yana cikin ‘yan wasan da ake ganin Guardiola zai dauko domin gyra bayansa. (Telegraph – subscription only)

Shugaban Barcelona Josep Maria Bartomeu ya yi watsi da yiyuwar dan wasan Paris St-Germainda Brazil Neymar, mai shekara 28, zai dawo Nou Camp amma ya ce yana diba yiyuwar dauko dan wasan gaba na Inter Milan da Argentina Lautaro Martinez, mai shekara 22. (TV3 via Mundo Deportivo – in Spanish)

Bartomeu ya kuma ce yana da “tabbataci” Lionel Messi, mai shekara 33, zai ci gaba da taka leda a Nou Camp har wuce badi. (TV3 via Evening Standard)

Real Madrid tana da kwarin guiwa kan dan wasan Faransa Kylian Mbappe, mai shekara 21, zai fara tattauna da Paris St-Germain kan batun komawarsa Madrid nan da shekara daya. (Marca)

Liverpool na tunanin sayar da dan wasan bayanta na Croatia Dejan Lovren, mai shekara 31, duk da ya nemi a tsawaita kwantaraginsa. (Goal)

Bayern Munich na shirin taya dan wasan TottenhamTanguy Ndombele, mai shekara 23, da kuma dan tsakiya na Faransa Tiemoue Bakayoko, mai shekara 25, daga Monaco. (Le10Sport via Daily Mail)

Nice ta taya dan wasan Sifaniya mai shekara 24 Rony Lopes daga Sevilla. (RMC Sport – in French)

Brentford na son dan wasan Portsmouthmai shekara 24 Ronan Curtis domin maye gurbinsa da dan wasan Algeria Algerian Said Benrahma. (The News, Portsmouth)

Dan wasan baya na Bournemouth Nathan Ake, mai shekara 25, ba zai sake buga wasa ba a wannan kakar saboda raunin da ya ji a wasa da Leicester. (Bournemouth Echo)

More News

Zanga-zanga: An jibge Æ´an sanda 4200 a Abuja

Rundunar Æ´an sandan birnin tarayya Abuja ta tura Æ´an sanda 4200 gabanin zanga-zangar da za a gudanar a cikin watan Agusta. Kamar yadda masu shirya...

Kamfanin NNPC ya shirya daukar karin ma’aikata

Kamfanin mai na Nigerian National Petroleum Company Limited ya shirya daukar karin ma’aikata.Kakakin kamfanin na NNPC, Olufemi Soneye, ya tabbatar da hakan a wata...

Ya kamata matasa su yi haÆ™uri zanga-zanga ba ita ce mafita ba – Sarkin Zazzau

Sarkin Zazzau, Mai Martaba Ahmed Nuhu Bamalli ya ce matasa su ƙara haƙuri da gwamnatin tarayya su janye zanga-zangar da suka shirya gudanarwa a...

Zanga-zanga: Tinubu ya gana da gwamnonin APC

Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya gana da gwamnonin da aka zaɓa ƙarƙashin jam'iyar APC. Taron ganawar da aka gudanar a fadar shugaban ƙasa ta...