Majalisun kasa sun amince da bukatar Tinubu ta ciwo bashin dalar Amurka biliyan $2.35

Majalisar kasa ta amince da bukatar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya gabatar a gabanta  ta neman gwamnatinsa ta ciwo bashin kudi dalar Amurka biliyan $2.35 domin cike giɓin kasafin kudin shekarar 2025.

Dukkanin majalisun biyu ta dattawa da kuma ta wakilai sun amince da bukatar ciwo bashin a ranar Laraba bayan da suka nazarci rahoton kwamitin majalisun kan bashin cikin gida da kuma na kasashen waje.

Har ila yau sun kuma amince da buƙatar shugaban kasar ta sayar da takardar lamunin Sukuk na dalar Amurka miliyan $500 a kasuwar hada-hadar kudade ta duniya domin samun kudin daukar nauyin samar da wasu ayyukan more rayuwa.

A farkon wannan watan ne a cikin wata wasika da ya aikewa majalisun Tinubu ya bukaci yan majalisun su amince da bukatar ciwo bashi wanda ya ce ya zama dole kamar yadda dokar kasafin kudin shekarar 2025 ta tanada.

Ya ce a cikin kasafin kudin shekarar 2025 an yi tanadin cin bashin naira tiriliyan ₦9.28 domin cike giɓin kasafin inda a ciki za a ciwo bashin naira tiriliyan ₦1.84  kusan dalar Amurka $1.229 daga ƙasashen waje.mjaa

More from this stream

Recomended