Majalisar Wakilai Za Ta Bincike Lamarin Rufe Kofar Majalisa Da DSS Suka Yi

[ad_1]

Majalisar wakilai ta ce abin kunya ne a ce jami’an tsaron sun rufe kofar majalisa sun hana ‘yan majalisar yin aikinsu musamman ganin yadda majalisar ita ce kashin bayan dimokradiyya.

“Mun yi Allah wadai da wannan abun da ya faru,” in ji Shehu Sale Rijau, dan jam’iyyar APC kuma dan majalisar wakilai mai wakiltar kananan hukumomin Magama da Rijau. Ya ce kwamitin zai yi kokarin gano musabbabin lamarin duk da cewa sun sani cewa ya na da nasaba da siyasa.

Ya ce wannan lamari ya kara hada kansu, “domin wadannan abubuwan da ‘yan jam’iyyun adawa ke yi, kokari ne na son bata wa jam’iyyarmu suna ko wannan gwamnatinmu.” Saboda haka ba za su yarda da wannan ba.

Sai dai Sanata Suleiman Hunkuyi dan jam’iyyar adawa ta PDP ya ce “Shiri ne na zamba,” wato na cin amanar dimokradiyyar Najeriya.

Ya ci gaba da cewa, “Idan ba haka ba,mene ne hujja? Wa ke da iko da zai zo ya hana a shiga ko a fita daga majalisa? Ya amsa da cewa, “mukarraban shugaban kasar Najeriya Buhari ne.”

Wasu masu fashin baki a al’amuran siyasa na ganin akwai abun dubawa a rudanin da ke neman raba kawunan ‘yan majalisar.

“Abu biyu ne ya haddasa wannan rikicin,” inji Kabir Ibrahim Tukura.

Tukura ya ce, na farko dai, suna ganin idan aka koma majalisa ta yi zama na duba kwarya-kwaryar kasafin kudi na hukumar zabe da aka gabatar, to ta iya yiwuwa tun da yanzu sanatocin APC suna da yawa, kuma ba a san iyakacin wadanda suke son dawowa ba, “don na san akwai masu son dawowar.”

“To akwai yiwuwar samun adadin wadanda za su iya tsige shugaban majalisa,” inji Tukura, wanda shine suke kokarin dakatar da faruwar hakan.

Ya ci gaba da cewa, dalili na biyu kuma ba wani abu ba ne sai don a bata wa Shugaba Buhari suna, a nuna wa duniya cewa ai mulkin kama-karya ya ke yi kuma ba ya adalci a Najeriya.

Shi kuma Dakta Abu Yazid cewa ya yi wannan rikicin ake yi bai zo da mamaki ba don abu ne da suka yi hasashen zai faru.

“Saboda akasarin mutanen dama can ‘yan PDP ne. Sun yi amfani da sunan Buhari ne domin samun matsayi.” inji shi.

Majalisar wakilai ta ce za ta katse hutunta a mako mai zuwa domin yin nazari kan kwarya-kwaryar kasafin kudi da shugaba Buhari ya aika masu.

Saurari cikakken rohoton

[ad_2]

More News

Kwankwaso ya bada tallafin miliyan ₦50 ga mutanen da ambaliyar Borno ta shafa

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam'iyar NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bada tallafin naira miliyan 50 ga mutanen da ambaliyar ruwa a...

Sakamakon NECOn 2024 ya fito

Hukumar shirya jarabawar ta kasa ta fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare ta watan Yuni/Yuli 2024, inda kashi 60.55 cikin 100 na waÉ—anda suka...

Ƴan Najeriya na shan baƙar wahala—Janar Abdulsalami

Tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalami Abubakar, ya ce wahalhalun da ake fama da su a Najeriya na kara tabarbarewa, kuma rabon kayan agajin ba...

EFCC ta musalta cewa Yahaya Bello na tsare a ofishin hukumar

Hukumar EFCC dake yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa ta'annati ta ce tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello baya ya tsare a hannunta. A...