Majalisar wakilai ta nemi gwamnatin tarayya da ta samar da tallafin maganin cutar kansa

Majalisar wakilai ta tarayya tayi kira ga gwamnatin tarayya da ta samar da tallafin maganin magunguna cutar sankara wato kansa.

Majalisar ta kuma yi kira ga gwamnatin tarayyar da ta sa a rika tantance cutar kyauta kana ta kara yawan cibiyoyin da ake kula da masu cutar tare da samar da injin da ake kona cutar da shi a dukkanin fadin Najeriya.

Majalisar ta zartar da kudirin ne yayin zamanta na ranar Laraba biyo bayan amincewa da kudirin da Aderemi Oseni dan majalisa daga jihar Oyo ya gabatar a majalisar.

Da yake gabatar da kudurin Oseni ya ce alhakin gwamnati ne ta tabbatar da samar walwala da kuma lafiyar yan kasa.

Ya ce cutar kansa na daga cikin manyan kalubale a fannin lafiya a Najeriya inda yawancin masu cutar basa iya biyan kudin maganinta saboda tsada.

Ya kara da cewa cutar na cigaba da yaduwa cikin sauri a Najeriya inda wani rahoto ya bayyana cewa a shekarar 2020 akwai yan Najeriya 125,000 da aka tabbatar suna dauke da cutar.

Dan majalisar ya ce irin cutar kansa da suka fi addabar yan Najeriya sun hada da ta mafitsara, nono  da kuma mahaifa.

More from this stream

Recomended