Majalisar Wakilai Ta Nemi a Dakatar da Ƙarin Cajis Na Cire Kudi a ATM da CBN Ta Ƙaƙaba

Majalisar Wakilai ta bukaci Babban Bankin Najeriya (CBN) da gaggauta dakatar da sabon karin kudaden cire kudi a ATM da kuma janye dakile cire kudi kyauta ga abokan huldar da ke amfani da na’urorin ATM na wasu bankuna daban.

‘Yan majalisar sun yi nuni da cewa karin kudaden cire kudi da CBN ta yi da kuma hana cire kudi kyauta ga abokan huldar da ke amfani da ATM na wasu bankuna zai kara wa ‘yan kasa nauyin kudi da ba dole ba.

Sun bayyana cewa wannan mataki ba shi da wata hujja, musamman ganin yadda bankuna ke samun riba mai yawa ba tare da inganta ayyukan da suke yi ko kayayyakin morewar kwastoma ba.

Majalisar ta bayyana damuwa cewa karin kudaden cire kudi zai hana talakawa shiga tsarin hada-hadar banki, abin da zai iya gurgunta manufofin CBN na fadada shigar kowa cikin harkokin hada-hadar kudade.

An cimma wannan matsaya ne bayan Marcus Onobun ya gabatar da kudiri a zaman majalisar da aka yi a ranar Talata.

Onobun ya jaddada cewa CBN ta sake duba sashe na 10.7 na dokar da ke jagorantar cajar kudaden ATM, wanda aka yi wa kwaskwarima a karon karshe a shekarar 2019, inda aka rage caji daga N65 zuwa N35 kan kowace mu’amala.

A cewar Onobun, sabon tsarin zai ci gaba da ba da damar cire kudi kyauta ga abokan huldar da ke amfani da ATM na bankunansu.

Sai dai ga wadanda ke amfani da ATM na wasu bankuna a cikin harabar banki, za a caje su N100 kan kowace N20,000 da suka cire. Haka kuma, wadanda ke cire kudi a ATM da ke wajen harabar banki, kamar a kasuwanni da manyan wuraren hada-hada, za a caje su N100 tare da karin N500.

Majalisar ta bukaci CBN da ta dakatar da aiwatar da wannan sabon tsari har sai an tattauna da kwamitocin da ke kula da harkokin banki, kudi, da cibiyoyin hada-hadar kudade.

‘Yan majalisar sun kuma nuna damuwa kan yadda matsin tattalin arziki ke kara dagule wa ‘yan kasa rayuwa, musamman sakamakon hauhawar farashi, karin kudin man fetur, hauhawar kudin wutar lantarki da kuma wasu caje-caje da ke rage yawan kudaden da mutane ke samu.

Majalisar ta nanata cewa dole ne gwamnati ta kare ‘yan kasa daga duk wani tsarin da zai kara jefa su cikin kuncin tattalin arziki.

More from this stream

Recomended