Majalisar wakilai na neman a riƙa daurin rai da rai ga masu shigo da jabun magani Najeriya

Majalisar wakilai ta tarayya na neman a riƙa ɗaurin rai da rai ga mutanen da suke shigowa ko kuma sarrafa jabun magunguna a ƙasar nan.

Ƴan majalisar na son Lateef Fagbemi ministan shari’a ya gabatarwa da majalisar gyaran dokokin  da ake da su domin tsaurara hukunci ga mutanen da aka samu da laifin samar da jabun magungunan.

Majalisar ta zartar da kudirin ne a yayin zamanta na Talata biyo bayan kudirin da ɗan majalisa, Muktar Shagaya ya gabatar gabanta..

Kudirin na zuwa ne biyo bayan yawan da ake samu na karuwar yaɗuwar jabun magunguna da kuma kayayyaki marasa inganci a yan shekarun nan.

A watan Disambar shekarar 2023 hukumar NAFDAC ta sanar da lalata jabun magunguna na biliyan naira biliyan 120 da aka samu cikin watanni 6 kacal.

Da yake gabatar da kudirin Shagaya ya ce tattalin arzikin Najeriya na asarar sama da naira tiriliyan 15 a duk shekara saboda jabun magunguna.

More from this stream

Recomended