Majalisar Dokokin Kano Ta Zartar Da Dokar Ƙirƙirar Masarautu Masu Daraja Ta Biyu

Majalisar dokokin jihar Kano ta zartar da wata doka da za ta samar da wasu masarautu masu daraja ta biyu a jihar.

Kudirin dokar da aka gabatar da shi a ranar Litinin ya tsallake karatu na ɗaya, na biyu da na uku a ranar Talata.

Kudirin dokar na son samar da masarautu uku da suka haɗa da Masarautar  Rano da ta ƙunshi(Rano,Bunkure, Kibiya)  Masarautar Karaye (Karaye da Rogo) da kuma Masarautar Gaya(Gaya Ajingi Albasu).

Masarautun masu daraja ta biyu za su kasance ƙarƙashin Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II.

Hakan na zuwa ne kwana guda bayan da babbar kotun jihar Kano ta haramtawa tuɓaɓɓen  Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero ayyana kansa a matsayin sarki har sai ta kammala ƙarar da take gabanta.

More from this stream

Recomended