Majalisar dokokin jihar Gombe ta zartar da dokar kafa hukumar kula da masu buƙata ta musamman

Majalisar dokokin jihar Gombe ta zartar da kudirin dokar da zai samar da hukumar  da za ta kula da da mutane masu buƙata ta musamman.

Dan majalisar jihar, Shu’aibu Haruna shi ne ya gabatar da kuɗirin dokar.

An bayyana yunkurin samar da hukumar a matsayin wani gagarumin cigaba wajen kare hakkin mutane masu buƙata ta musamman da kuma tabbatar da cewa an dama da su dai-dai wadaida a al’amuran Najeriya.

An amince da zartar da kudirin ne bayan da kwamitin majalisar kan harkokin mata da cigaban al’umma ya miƙa rahotonsa ga majalisar kan batun.

Gabriel Galadima Fushion ɗan majalisa mai wakiltar Kaltungo wanda shi ne shugaban kwamitin ya ce an tsefe kudirin dokar domin ganin tayi dai-dai da bukatar mutanen jihar.

More from this stream

Recomended