Majalisar Dokokin Jigawa Ta Fara Bincike Kan Kwantiragin Asibitin Kiyawa

Majalisar Dokokin Jihar Jigawa ta umarci kwamitin lafiyarta da ya fara gudanar da bincike kan kwantiragin da aka bayar na mayar da Asibitin Kiyawa daga cottage hospital zuwa cikakken asibiti gaba ɗaya.

Shugaban kwamitin lafiya na majalisar, Hon. Usman Abdullahi Tura, ne ya bayyana haka ga manema labarai a ranar Alhamis.

Ya ce matakin ya biyo bayan korafe-korafe da kwamitin cigaban al’ummar Kiyawa ya gabatar kan yadda kamfanin da ke aikin ya gudanar da kwantiragin.

Tura ya bayyana cewa majalisar dokokin jihar ƙarƙashin jagorancin Kakakin majalisar, Rt. Hon. Haruna Aliyu Dangyatin, ta bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan kwantiragin da ya shafi gina sabuwar asibiti, kawo kayan aiki da kuma girkawa cikin gaggawa.

A cewarsa, an bai wa kwamitin lafiyar ikon ziyartar wurin aikin don tantance yadda aka bayar da kwantiragin, yadda ake aiwatar da shi da kuma gano matsalolin da suka taso da abin da ya faru ainihi a aikin.

A baya-bayan nan Gwamna Malam Umar Namadi tare da Kakakin Majalisar sun kai ziyara Asibitin Kiyawa a yayin taron tattaunawa da jama’a da aka gudanar a garin. A lokacin, al’ummar yankin sun koka kan yadda aikin ya kasance.

Dan majalisar da ke wakiltar mazabar Guri ya tabbatar da cewa a yayin wannan ziyara, an gano wasu matsaloli da suka shafi tsarin gine-ginen asibitin.

More from this stream

Recomended