
Majalisar dokokin jihar Benue ta dakatar da mambobinta su hudu kan zargin da ake musu na kitsa tsige shugaban majalisar, Aondona Dajoh.
Gidan talabijin na Channels ya bada rahoton cewa yan majalisar da aka dakatar sun hada da Alfred Berger dake wakiltar al’ummar, Makurdi north,Terna Shimawua dake al’ummar, Kiran, Cyril Ekong na obi da kuma James Umoru dake wakiltar al’ummar mazabar APa.
Majalisar ta yanke hukuncin dakatar da yan majalisar 4 ne a zaman da tayi na ranar Juma’a.
Saater Tiseer, shugaban masu rinjaye na majalisar ne ya gabatar da kudirin dake bukatar sauraron gaggawa.
Tiseer ya zargi yan majalisar da kokarin tayar da rikici a majalisar ana zaune kau.
Daga bisani Dajoh ya umarci dan sandan majalisar da ya fitar da dakatattun yan majalisar daga harabar majalisar.
Shugaban majalisar ya sanar da nadin, Audu Elias a matsayin sabon mai magana da yawun majalisar muƙamin da a baya Berger ke rike da shi.